Yadda Ake Ma Saurayi Shagwaba a Soyayya – Shagwabar budurwa – Shagwabar Amarya Da kukan Shagwaba 2023

Yadda Ake Ma Saurayi Shagwaba a Soyayya – Shagwabar budurwa – Shagwabar Amarya Da kukan Shagwaba 2023

Yadda Ake Ma Saurayi Shagwaba a Soyayya: yawan cin mata yanzu suna son yima samari shagwaɓa musamman indan saurayin yana son budurwar sosai sai ta fara yi ma saurayin shagwaɓa cikin salo mai jan hankali. Wasu samari sukance suna son sanin kalolin shagwaba amfaninta to ya kamata ku sani Akwai hanyoyi da yawa wadanda mata ke bi wurin yiwa samari shagwaɓa a sauwake cikin nishadi da farin ciki.

Saboda haka a wannan rubutun za muyi cikakkun bayanai akan abubuwan da Suka shafi shagwaɓa, kamar yadda kuke tambayoyi irin kukan shagwaba, shagwaba a waya, yadda ake ma saurayi shagwaba a waya, shagwaba a soyayya, shagwabar budurwa, kalaman shagwaba, yadda akewa saurayi shagwaba, yadda akema saurayi shagwaba, ya ake shagwaba, shagwabar amarya, iya shagwaba da dai sauransu.

Menene Shagwaɓa A Soyayya

A matsayin ki na budurwa yana da matuƙar amfani kisan lokacin da masoyin ki yake cikin farin ciki, Domin a wannan lokacin ne ya dace kiyi masa shagwaba. saboda hakan zai kara shaƙuwa a tsakaninku mai yawa wacce bazata misaltu ba. To amma domin sanin yadda ake ma saurayi shagwaɓa da kuma sanya shi farin ciki, to kinzo wurin da ya dace. Yanzu ki/ku cigaba da karanta wannan rubutun nawa taƙaitacce domin ki aka yi shi.

Shagwaɓa a cikin soyayya tsakanin saurayi da budurwa abune mai matuƙar amfani sosai domin yana kara shaƙuwa da farin ciki tsakanin masoya baki Daya. Shagwaɓa a soyayya ana bayyana ta da yin abubuwa tsakanin masoya biyu dan kara shaƙuwar soyayyar su a koda yaushe. Hakan yana faruwa ne ta hanyar yin wasu abubuwa wanda zai sa saurayi ya fahimci cewa budurwa tana sonshi kuma tana buƙatar kulawa daga gareshi sosai.

Duk soyayyar da ake yin shagwaɓa tsakanin masoya biyu, musali ace  masoya na jin kunyan junan su, to wannan shagwaɓar dake tsakaninsu zai basu damar iya gayawa juna sirrinkansu a sauwaƙe ba tare da jin kunya ba. Kuma mafi yawancin ƴan mata a yanzu suna yawaita yi wa samarin su shagwaɓa domin su gane irin san da suke masu ko kuma samun wani abu mai daraja, kuma suna samun nasara sanadin soyayya.

 Abin ban sha’awa akan shagwaɓa. Domin kuwa Mata kala-kala ne kuma Mata suna da salo salo da ban da ban na wurin bayyana shagwaɓa ga samarin su a kowani lokaci. Saboda yanzu Idan mace nasan abu wajen saurayin ta, kafin tasamu abunda take so a wasu lokutan dole sai ta yiwa saurayin ta shagwaɓa kafin ya iya bata wannan abun batare da yasan yana badawa ba. ba sihiri bace kawai iyawace.

Yanzu Wasu mazan suna ganin cewa idan budurwa bata yiwa saurayin ta shagwaɓa, dan hakan yana nuna cewa bata son shi ko kadan. Idan akwai shagwaɓa, toh akwai yarda da juna cikin soyayya sannan kuma akwai nishadi da farin ciki. Mafi yawanci idan saurayi yana cikin damuwa ko ɓacin rai, shagwaɓa daga wajen budurwar dake ƙaunar sa zai iya tasirin kauda halin da yake ciki na damuwa. 

Soboda Wadannan dalilan, shagwaɓa a soyayya tana da amfani a rayuwar masoya fiye da yadda ake tunani, Ammafa sai Wanda yake soyayya zaifi fahimtar hakan.

Yadda Ake Ma Saurayi Shagwaba a Soyayya
Yadda Ake Ma Saurayi Shagwaba a Soyayya

Anfanin Shagwaɓar Budurwa Ga Saurayin Ta

Shagwaɓar Budurwa: Abunne dake kawar da damuwar saurayi cikin sauki ba tare da shan wahala ba. Kuma ga wani dalilin, kunsan dariya tana da daɗi, kuma dariya tare da wani tafi daɗi. A koda yaushe saurayi da budurwa muna so mu kasance tare da mutanen da za su iya sa mu dariya, wato bamu farin ciki. musamman idan suna taimaka mana mu yi dariya tare, akan abubuwan da ke sakamu bakin ciki, su kuma sai su rarrashe mu cikin salo. 

Karku manta akwai hanyoyi masu yawa domin jin daɗin rayuwar soyayya. Abun tambaya anan shine me ya sa mutane ke daraja abin dariya fiye da, a ce, zama ƙwararren mai dafa abinci? Karkuyi dariya saboda idan muka kalli Shagwaɓa. To ga namiji wannan yana ɗaya daga cikin mafi kyawun hanyoyin ƙarfafa dangantakar ki dashi. Domin kun kasance tare da juna sanadin soyayya na sama da shekara ɗaya ko biyu, hmm, to hakan ba yana nufin ba za ku iya yin shagwaɓa ba a cikin soyayyaba. Sai dai muce kune kukafi samun damar yin shagwaɓa ga juna, saboda wannan dalilin na fahimtar juna.

Idan kun so koda yaushe kuna iya yiwa juna shagwaɓa ta hanyoyi daban-daban. Domin wannan zai taimaka muku wajen kiyaye matsala a cikin dangantakar ku. Shagwaɓar budurwa ga saurayin ta yana da matuƙar anfani sosai ko kuma ace shagwaɓar Amarya ga mijinta yana da matuƙar anfani sosai a wurin gudanar da zaman takewa na yau da gobe, musamman ma a wannan zamanin. 

Shagwaɓar mace a soyayya, abu ne wanda zamu kira kmar sinadarin soyayya ko zamantakewa, domin yin ta a soyayya yana da mahimmanci ba wai jindaɗi ba kawai tsakanin masoya ba, Sai dai tana taimakawa wajen kara ƙarkon soyayya da zaman aure ga ma’aurata. Shagwaɓa a ko ina tana da matuƙar anfani wanda ba zamu kididdige ba kai tsaye. Sannan kuma shagwaɓar mace ko shagwaɓar budurwa ma takan  haifar da wasu halaye na musamman. 

Shagwaɓa a kaice tana nuna Waɗannan kyawawan halayen, girmamawa tsakanin masoya, rarrashi, tana nuna rashin gajiyawa, Kuma tana sanyaya rai.  Dukkan waɗannan abubuwane dake da tasiri sosai ba kaɗan ba wajen kara cusa soyayya a zuciyan saurayi da budurwa. 

Duk daga cikin anfanin shagwaɓar budurwa ga saurayin ta, akwai abubuwa kamar haka:

shagwaɓar mace na maida zuciyan saurayi ya narke a soyayya, yaji babu abunda yake son ya gani sai masoyiyarsa ta hakiƙa. Saboda zai ɗauki shagwaɓar da anfani sosai.

Shagwaɓar budurwa yakan kawo kusanci ko shigar da mace zuciyan saurayin ta, kuma duk yawancin lokacin da ya tuna da ita sai yaji wani daɗi a ran sa.

Shagwaɓar budurwa: tana matuƙar taimakon budurwa wajen samar da amincewa tsakaninta da saurayinta. Kuma Saboda sanadiyar shagwaɓar budurwa ga saurayinta, domin kuwa duk masoya suna jin daɗi da kuma amincewa ko yarda da junansu sosai.fiye da yadda wasu za suyi tsammani daga Shagwaɓar budurwa a soyayya.

Anfanin shagwaɓar mace ga saurayinta shagwaɓar mace yawanci tana kauda zargi a soyayya tsakanin namiji da mace. To saboda haka yanzu zamu iya cewa idan soyayya ta kasance akwai shagwaɓa mai yawa daga ɓangaren mace ko budurwa to abune mai daɗi sosai. Saboda acikin irin aikin da shagwaɓar mace take ga namiji tana kauda hankalin saurayin daga zarginta koda kuwa tana yin wani abun da bai kamata ba a cikin soyayyar su to shagwaɓa zai taimaka wajen rufe sirrinta.

Kuma hakane yasa yawancin mace mai shagwaɓa idan tana soyayya da namiji yana daukan lokaci kafin saurayi ya fahimci tana yaudarar shi ne. Shagwaɓar mace tana haifar da Amana, Gaskiya, Kawaici, Yarda da juna, nuna soyayyar mace ta hakiƙa, Kuma tana sadaukar da rai ko jiki, Sannan tana kawar da kunci a zaman aure, da kuma rashin son kai ga juna.

Shagwaɓa A Soyayya: shagwaba a soyayya tana da amfani sosai, kamar shagwaɓar budurwa da saurayi, sanan tana sanya kusanci tsakanin ta da saurayi. A ƙullum saurayin da ya fahimci soyayya itace ke zama kauna to za kuga yana son ya ga masoyiyarsa tare da shi tana yi masa shagwaɓa a soyayya kamar wata karamar yarinya cikin salo na kamar yaudara to a koda yaushe dole zai ji ba daɗi idan babu ita a kusa da shi, saboda shagwaba a soyayya da take yi masa idan suna waya ko kuma a zaune wuri daya.

Salon Shagwaɓa: Salon Shagwaɓa Yadda Ake Ma Saurayi Shagwaɓa

Salon Shagwaɓa: Bayan sanin amfanin Shagwaɓa a soyayya, yanzu kuma zamu duba ɓangaren yadda ake yin shagwaɓar wato salon shagwaɓa a soyayya tsakanin masoya. Tanan ɓangaren akwai hanyoyi da dama da masoyiya zata iya ma saurayin ta shagwaɓa cikin birgewa amma a wannan taƙaitaccen rubutun nawa zanso na kawo muku salon shagwaɓa a soyayya guda Goma (10).

1). Ki Ɗauki Hoto Mai Ban Dariya

Ɗaukar hoto mai ban dariya idan kika nuna wa saurayin ki musamman idan ya bukaci ki turo masa hotonki saboda itama wannan wata salon shagwaɓar ce wacce ke kara shaƙuwa tsakanin masoya. ga mace wacce take neman sanin yadda akema saurayi shagwaɓa to ki bi wannan hanyar mai sauki a soyayya. 

Idan ya ga hoton kin yi shi cikin ban dariya, hakan zai sa shi yafara maki dariya kuma hakan zai sa shi cikin farin ciki. Daga nan sai ki tambayeshi me yasa yake dariya ko hoton baiyi kyau bane. Idan yace yayi kyau sosai, sai ki marairaice ki fara magana cikin salon shagwaɓa kina cewa shine kake yi mun dariya kuma bayan hoton yayi kyau, kuma kaine kace nayi daga nan shi kuma zai kara yin kasa da murya yana lallashin ki kamar kwai. Kuma idan kika yi wannan salon shagwaɓa zaiji ya kara sonki sosai idan har masoyi ne mai son soyayya da gaskiya. Dole kuma zai yabi kyawun ki ta yanda kema zai faranta miki sosai.

2). Kibashi Suna Mai Na Dariya

Acikin soyayya yan mata ya kamata su san cewa Maza na matuƙar son suga budurwa ta kira su da wani suna daban wanda basu taɓa kiran su da shi ba. Kuma wannan sabon salon shagwaɓar yafi aiki sosai musamman lokacin da kike son saurayin ki ya miki abunda kike ganin kamar bazai iya yi miki, to sai ki gwada wannan salon shagwaɓa.

Abu na farko idan kika kira saurayin ki da sunan ban dariya kuma wanda yake da alaka da soyayya, to wannan zai sa dukan ku farin ciki musamman saurayin daga nan kinga kin samu hanyar da zaki tambayeshi cikin shagwaɓa. Kuma har ma yayi miki abun fiye da yadda kike tunanin zai yi. Domin haka yana da matuƙar amfani kisan yadda ake ma saurayi shagwaɓa domin karban wani abu mai daraja. 

Abu mai mahimmanci kafin kiyi hakan, sai ki fara kwantar da hankalin ki sosai kisan irin abubuwan da yake so, Kuma ki gane cewa yana cikin farin ciki daga nan ne zaki iya sanin suna mai daɗi da zaki saka mishi. Kamar a misali idan mutum ne mai san kwallo saurayin, sai ki kira shi da sunan dan kwallon da yafi so, daga nan cikin salo sai ki nuna mai kina kishi da hakan a shagwaɓe.

3). Ki Bata Masa Lokaci

A Salon shagwaɓa Idan saurayi yana son ki har zuciyar sa da gaske, ko me kika yi a wurin shi hakane dai’dai, Kamar idan ysce zaku fita shopping, wajen shakatawa ko ziyara yace maki karfe 4 zai zo kuje, sai yazo karfe 4 ke kuma kice masa wania zaki shiga yanzu Idan kin fito kuma za kiyi kwalliya ya bari sai karfe 4, ki fada masa cikin shagwaɓa da kin bayyana dalili, to idan kikayi sa’a shi kenan kin samu wata dama, kinga shagwaɓar tasa makwullin soyayyar ta dawo hannun ki sai yadda kika juya shi. Amma idan bakiyi nasara ba ki samu matsala dashi saboda haka. Amma da kamar wuya koda shi ustaz ne. 

Dama soyayya budurwa itace Sarauniya mai juya masarautar Amma kuma a waje za kuyi tunani sarki shine mai mulki. Sannan duk Budurwa matsayin sarauniya take a soyayya, kuma komai ta yanke, ya zauna.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button