Saboda Zargin ɓatanci ga musulunci MURIC ta nemi a haramta fim din Nancy Isime

Kungiyar kare hakkin musulmi, MURIC ta Najeriya yi kira da a haramta wani fim da ake shirin fitowa da shi inda fitacciyar jaruma a Kudancin Najeriya Nancy Isime da wasu ’yan fim suka sanya cikakken sutura ta musulunci, sun sanya zumbulelen Hijabi ,da naqabi da safa sannan suka boye muggan makamai masu hadari.

Kannywood News A Yau, Ta ruwaito Kungiyar ta bayyana fim din a matsayin ‘shaidanci’, inda ta kara da cewa yana nuna mata musulmi a matsayin masu aikata laifuka ko ƴan ta’adda wanda yin hakan kuma tunzura jama’a ne su ƙyamaci addinin musulunci.

A cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun Babban Daraktan MURIC, Farfesa Ishaq Akintola, a yau Alhamis ya buƙaci hukumomi su dakatar da fim din

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button