Yanzu haka bisa jajircewar su, ƴan sanda a Katsina sun kama mutane biyu
GWANIN SHA’AWA: Yanzu haka bisa jajircewar su, ƴan sanda a Katsina sun kama mutane biyu da ake zarginsu da hannu a garkuwa da mahaifiyar mawaki Dauda Rarara.
Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta kama wasu mutane biyu da ake zargi da yin garkuwa da mahaifiyar fitaccen mawakin nan, Dauda Kahutu aka Rarara.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Katsina, ASP Abubakar Sadiq Aliyu, a wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a, ya ce hukumomi na yi wa mutanen biyu tambayoyi.
“A yau Juma’a, 28 ga watan Yuni, 2024, da misalin karfe 0130, an samu bayanai a hedikwatar ‘yan sanda ta Danja.
Wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun mamaye gidan wata Hauwa’u Adamu mai shekaru 75 a kauyen Kahutu, karamar hukumar Danja, jihar Katsina, inda suka yi garkuwa da ita.
“Bayan samun rahoton ba tare da bata lokaci ba DPO Danja ya jagoranci tawagar jami’an tsaro zuwa wurin da nufin kamo masu laifin tare da kubutar da wanda abin ya shafa.
Wane fata za kuyi musu?