Martanin Governor Abba Kabir Yusuf Mai Zafi Kan Bullar Wata Kungiya Mai Tallata Auren Jinsi.
Martanin Governor Abba Kabir Yusuf Mai Zafi Kan Bullar Wata Kungiya Mai Tallata Auren Jinsi
Gwamnatin jihar Kano ta kaddamar da bincike kan jita-jitar yaduwar wata kungiya mai tallata auren jinsi a jihar Gwamnatin ta bukaci al’umma su kwantar da hankalinsu inda ta ce ba za ta taba barin irin wannan iya shege a jihar ba Hakan ya biyo bayan bullar wata kungiya mai suna ‘WISE’ da ta dade tana tallata auren jinsi wurin fakewa da wasu ayyuka
Gwamnatin jihar Kano ta yi martani kan bullar wata kungiya da ke tallata auren jinsi a jihar. Gwamnatin jihar ta tabbatar da samun labarin kungiyar da ake kira ‘WISE’ inda ta ce ta kaddamar da bincike kan lamarin. Gwamnatin jihar Kano ta fara bincike kan kungiyar ‘WISE’ da ake zargi da tallata auren jinsi.
Hadimin gwamnan a bangaren sadarwa, Hassan Sani Tukur shi ya tabbatar da haka a shafinsa na X a yammacin yau Lahadi 7 ga watan Yulin 2024.
Hassan ya ce gwamnatin ta tabbatar da cewa ba za ta amince da duk wani iya shege makancin haka ba a jihar.
“Gwamnatin jihar Kano ta samu labarin wata kuniya da ke tallata auren jinsi tun jiya, tuni aka kaddamar da bincike kan lamarin.” “Muna mai tabbatarwa ‘yan Kano cewa gwamnatinmu da ma wata gwamnatin mai zuwa a gaba ba za ta lamunci irin wannan iya shege ba.”
“Muna mai kiran jama’a da su kwantar da hankalinsu, gwamnati ta dauki matakai kan lamarin.”
Kungiyar mai suna Women Initiative for Sustainable Empowerment and Equality (WISE) ta dade tana gudanar da ayyukanta a jihar, cewar Kano Times. Kungiyar wacce ba ta gwamnati ba karkashin jagorancin Nnedinma Ulanmo tana da ofishinta mai lamba 239 a Jigirya Yankaba Kawaji, Bompai da ke jihar Kano.
Ayyukan kungiyar ya kara fitowa fili ne a ‘yan kwanakin nan yayin da ake ci gaba da cece-kuce kan yarjejeniyar Samoa.