BBC Hausa: Kalli Sunayen mutum 15 da gwamnatin Najeriya ta ce suna taimakawa Yan Ta’adda
BBC Hausa Kalli Sunayen mutum 15 da gwamnatin Najeriya ta ce suna taimakawa Yan Ta’adda
BBC Hausa: Gwamnatin Najeriya ta fitar da jerin sunayen mutum 15 waɗanda ta ce ana zargin su wurin taimakawa ta’addanci a ƙasar ta.
Ta ce kuma waɗanda ake zargi da taimakawa ta’addancin a kasar sun kunshi mutum tara da kuma wasu masu kamfanonin canji a kasa.
Rahoton daga NFIU ya nuna cewa kwamitin sa ido kan takunkumi a Najeriya tayi zama ranar 18 ga watan Maris, Kuma an bayar da shawarar saka takunkumi kan wasu mutane da cikin su da kuma kamfanoni saboda hannun da suke dashi gun tallafawa ta’addanci.
Mamu ya tallafawa ta’addanci sosai ta hanyar karɓar kuɗi da ya kai Dollar amurika $200,000 daga hannun waɗanda aka yi garkuwa da ƴan uwansu harda kai wa masu garkuwa, domin sakin fasinjojin jirgin ƙasan na Abuja zuwa Kaduna.
sannan kuma, rahoton ya ce ɗaya daga cikin mutanen da ake zargi kuma shi ne wanda ya kai hari kwanaki kan cocin Katalika na St. Francis da ke Owo, ta jihar Ondo ranar 5 ga watan Yulin, shekarar 2022.
Sannan an bayyana ɗaya daga cikin mutanen a matsayin member na ƙungiyar Ansarul Ansarul Muslimina Fi Biladissudam, Wanda ke alaƙa da Al-Qaeda da ke yankin Maghreb.
Kuma akwai wani babban kwamandan ƙungiyar na ISIS a Afrika ta Yamma, wanda shi ma ake zargi da taimakawa ta’addanci a Najeriya.
Gwamnatin Tarayya ta fidda sunayen Mutane da kamfanonin dake ɗaukar nauyin ƴan ta’adda a Nijeriya.
- Tukur Mamu
- Yusuf Ghazali
- Muhammad Sani
- Abubakar Muhammad
- Sallamudeen Hassan
- Adamu Ishak
- Hassana-Oyiza Isah
- Abdulkareem Musa
- Umar Abdullahi
- West and East Africa General Trading Company Limited
- Settings Bureau De Change Ltd
- G. Side General Enterprises
- Desert Exchange Ventures Limited
- Eagle Square General Trading Company Limited
- Alfa Exchange BDC