Na Fice Daga Addinin Kiristanci Saboda Na Lura An Maida Coci Dandalin Neman Kuɗi”-_Inji- Ugezu
“Na Fice Daga Addinin Kiristanci Saboda Na Lura An Maida Coci Dandalin Neman Kuɗi”-_Inji- Ugezu
Fitaccen ɗan fim kuma darakta a finafinan Kudancin Najeriya Nollywood , ya fice daga addinin Kirista ya koma addinin gargajiya, saboda a cewar sa yanzu a coci neman kuɗi ake yi, ba ibada ba.
A wata tattaunawa da Majiyar Karaduwa Post, Jaridar Focus News Hausa, Ta Jiyo Mana Ugezu ya ce yanzu addinin Kirista ya koma neman kuɗi muraran. “An saki koyarwar Linjila. Kamar yadda na taɓa karantawa a wani rubutu da Chimamanda Adichie ta taɓa yi a baya, inda ta bada labarin ta je taron rufe wata gawa a Cross Riba, amma Limanin Coci ya ce ba za a rufe gawar ba, saboda ana bin mamacin bashin kuɗin taimakon coci da ya ƙi biya.”
Ya ce amma har yanzu ya na zuwa Coci idan abokan sa Kirista sun gayyace shi wani buki haka.
Sai dai ya ce ya kama addinin gargajiya gadan-gadan bayan ficewar sa daga addinin Kirista.
Ugezu ya shawarci ƙabilar Igbo ‘yan uwan sa su rungumi addinin gargajiya domin warware matsalolin da ke damun su.
“Na taɓa jin cewa a garin Aguata ana cikin waƙe-waƙe a Coci sai wasu yara guda biyu suka shiga Cocin a guje, suka shaida masu cewa ga ‘yan bindiga nan makiyaya ɗauke da bindigogi AK-47. Nan da nan kowa ya arce daga Cocin. To ka ga idan garin da ake bin addinin gargajiya ne na Odinani a ƙabilar Igbo, babu wanda zai tsere.