Cikakken martanin mutane akan rokon Addu’ar mutane da Dauda Kahutu Rarara yayi.

Yau Mawaki Rarara ya bukaci jama’a su sanya mahaifiyarsa a cikin addu’o’in sallar jumma’a bayan da ‘yan bindiga sun sace ta.

Amma Kuma sai Suka bayyana wani abun mamaki Wanda Ba’ayi Tsammani Ba.

Na zubda hawaye da irin comment da naci karo da shi mutane keyi a ƙarƙashin jaridu da aka sanar da garkuwa da mahaifiyar Mawaƙi Dauda Kahutu Rarara. Sannan Kuma Yana rokon Addu’a.

Kaso 90 cikin ɗari na masu kwament suna nuna jin dadinsu da garkuwa da mahaifiyar Mawaƙin

Sai na zauna shiru nake tunanin me ya kawo haka. Sai zuciyata take karanta mun yana da alaƙa da irin kalaman da Dauda Kahutu keyi don gyara kashin meyarsa a wajen Tinubu..

A watannin baya Dauda Kahutu yayi maganganu akan sha’anin tsaro har yake bayyana cewa, “An sami tsaro sosai a lokacin Tinubu sama da lokacin Buhari.

Sai zuciyata take fada mun wataƙila yana da alaƙa da wannan yasa mutane ke furta munanan kalamai akan ibtilain da ya faru da mahaifiyar Rarara

Da Farko muna mika sakon Allah ya bayyanata ya kare faruwan haka gaba.

2: Wannan lamari na garkuwa da mutane ya isa ya zama darasi ga manya Najeriya da masu ɓoye gaskiya don gyara kashin miyarsu su gane cewa, Allah baya Bacci.

Allah yana da hanyoyi daban-daban na kama ɗan adam..Allah ya kawo mana zaman lafiya a kasar mu Najeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button