Abunda yake bani haushi da yayana G-Freah kamar yadda yake yawan yin Karya.
“G Fresh Al’Amin yayana ne uwar mu ɗaya ubanmu ɗaya, amma babu abinda yafi ban haushi a rayuwa ta kamar yadda yake yawan yin ƙarya.
Yace wai ya karanci aikin jarida kuma karya yake nine na karanci aikin jarida shi daga Secondary ya tsaya.
Shi kansa sunan da yake anfani dashi ba nasa bane, suna na ne, shi sunan sa Abubakar nine Al’Amin, kuma yace wai kakan mu ne Al’Amin nanma ƙarya yake.
Duk sanda mukai waƙa baya ambatar suna na, wata ma da kuɗina ake anfani amma Saiya ɓoye suna na ya tallata kansa kaɗai.
A matsayin sa na yayana fatan da nake shine kada ya mutu a haka, ina fatan ya tuba ya koma ga Allah kuma ya canja daga maƙaryaci ya rinƙa faɗin gaskiya.
~ Cewar ƙani ga G Fresh Al’Amin Kano State Material, Mai suna Al’Amin G Fresh, a tattaunawar sa da Dala FM